Sojoji 35 Da Fursunoni 10 Sun Kamu Da Korona A Bauchi

0
222

Kwamishinan lafiya na jihar Bauchi Dakta Aliyu Muhammmad Maigoro ya shaida cewar sojoji 35 da kuma Fursunoni 10 ne suka tabbatar suna dauke da cutar Korona a gwajin da suka yi a baya-bayan nan.

Kwamishinan ya shaida hakan ne a jiya sa’ilin ganawar mako-mako da gwamantin jihar ke yi da manema labaru don shaida wa duniyar halin da ake ciki kan annobar a matakin jiha.

Yana mai cewa sojojin da suka kamu da cutar sun zo jihar Bauchi ne domin gudanar da wani aiki na musamman inda aka killacesu kana aka yi musu gwaji, yana mai cewa a bisa haka ne aka samu mutum 35 da su ke dauke da cutar daga cikin adadin mutum 69 da aka gano suna dauke da cutar Korona a ranar Talatar da ta gabata.

Ya kuma kara da cewa daga cikin su an samu tabbacin Fursunoni 10 sun kamu da cutar, sai kuma wasu da suka kamu da cutar mutum 15 da aka gano sun yi mu’amala da mataimakin gwamnan jihar wanda ya kamu da cutar a kwanakin baya.

Har-ila-yau kwamishinan lafiya na jihar ya kuma shaida cewar mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Sanata Baba Tela ya warke daga cutar Korona bayan da ya kamu da cutar  kwanakin 10 da suka gabata.

Har-ila-yau, hukumomin sun kuma shaida cewar tun bayan warkewar mataimakin gwamnan wanda shine shugaban kwamitin yaki da Korona a jihar tunin kuma aka sallameshi daga cibiyar killacewa.

Sai dai kuma cikin alheni da bakin ciki hukumar ta sanar da cewa cutar ta kashe wani kwararren Likita a jihar.

Maigoro ya sanar da cewa sun fitar da sabbin tsare-tsare da zai basu damar dakile bazuwar cutar. Ya bada tabbacin cewar kwamitin yaki da cutar zai sake jan damara domin tabbatar da rage kaifin cutar tare da shawo kan cutar.

Shi ma a jawabinsa, shugaban hukumar lafiya a matakin farko na jihar Bauchi (BASPHCDA), Dakta Rilwanu Muhammad ya shaida cewar an samu adadin mafi tsoka na wadanda suka kamu da cutar ne tun bayan janye dokar kulle a jihar.

Ya na mai cewa zuwa yanzu jihar tana da cibiyoyin killace masu cutar da su ke shake da kayan jinya tare da wadattun kayayyakin jinya, sai ya ke mai tabbatar da cewar suna da karfin magance cutar.

Ya sanar da cewa dakin gwaje-gwajen cutuka a jihar na aiki gadan-gadan, inda ya ke mai cewa dukkanin gwajin cutar yanzu an samu saukin hanyoyin yinsa ba tare da sai an kai Abuja ko Jos kafin a samu sakamako ba.

Ya bada tabbacin kwararrun jami’ansu na bin sahu da dindigin wadanda ake zargin sun yi mu’amala da masu cutar domin gwada su.

Rilwanu yana mai cewa tun bayan janye dokar hana zirga-zirga a jihar jama’a sun koma gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba tare da kiyayewa da bin ka’idojin dakile bazuwar cutar ba, sai ya nuna hakan a matsayin abun bakin ciki da ya nemi a shawo kan lamarin.

Da ya ke jawabinsa gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya nuna alheni kan likitan da ya rasu a sakamakon cutar, yana mai shaida cewar dile jama’an jihar su baiwa gwamnati hadin kai dari bisa dari domin tabbatar da shawo kan wannan matsalar ta korona.

Ya na mai sanar da cewa za su yi dukkanin abinda ya dace wajen cigaba da kiyaye rayuka da dukiyar jama’an jihar inda ya nemi hadin kan jama’a kan hakan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here