Shugaba Buhari zai yiwa yan Najeriya bayyani gobe Juma’a

0
129

Daga Hannatu Sulaiman Abba

Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari mai ritaya, Zai yi jawabi a ranar Juma’a gobe don gabatar da jawabi ga al’ummar kasar a bikin tunawa da ranar Dimokiradiyya ta bana.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis ta mai ba shi shawara ta musamman kan harkokin yada labarai da yada, Femi Adesina, za a watsa sakon Shugaban kasar ne da karfe 7 na safe.
Sanarwar ta kara da cewa, “Don tunawa da ranar Dimokiradiyya ta Najeriya, Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yiwa al’ummar kasar jawabi aranar Juma’a, 12 ga Yuni, 2020, da karfe 7 na safe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here