Korona tasa yan fim munyi mutuwar tsaye, inji Adama matar Kamaye a wasa

0
758

FITACCIYAR jaruma Hajiya Zahra’u Saleh, wadda aka fi sani da Adama matar Kamaye ta cikin shirin ‘Daɗin Kowa’ na gidan talbijin na Arewa24, ta bayyana halin da ta shiga sakamakon killace ɗan ta da aka yi a kan ya kamu da cutar korona (Covid-19).

Jarumar ta bayyana hakan ne a tattaunawar da ta yi da mujallar Fim.

Zahra’u ta fara bayani ne da yadda cutar ta ragargaji Kannywood, ta durƙusar da kowa.

A cewar ta: “A gaskiya, mu ‘yan fim mun samu kan mu a cikin wani yanayi dangane da zuwan wannan cuta ta Covid-19, domin kuwa duk wasu harkoki namu sai da cutar ta tsayar da su, musamman dai yadda ake gudanar da ayyukan masana’antar.

“Sai ya zamo an daina komai, sai zaman gida. Duk da dai cewar al’amarin na duniya ne, amma mu ‘yan fim abin ya fi yi mana illa saboda babu yadda za mu gudanar da harkokin ba tare da mun taru waje ɗaya ba, to sai kuma aka ce an hana taruwa a waje ɗaya, kuma mu komai namu sai an taru.

“Da man can kafin a fara zaman gidan harkar ta shiga wani yanayi, to da Covid-19 ta zo sai aka ƙarasa mu gaba ɗaya, don haka sai mu ka yi mutuwar tsaye.”

Ta ci gaba da bayyana yadda cutar ta shafe ta kai-tsaye, inda ta ce: “Sai dai duk da halin da ake ciki a lokacin na labarin Covid-19 na ke ji, to kawai sai na ji ta zo mini har gida, domin kawai ina zaune a cikin gida kawai sai aka bugo mini waya daga Gombe, aka sanar da ni an killace ɗa na da ya dawo daga Abuja saboda ya na ɗauke da Covid-19.

“Nan fa na ƙara shiga tashin hankali, domin a lokacin sai na ji kamar ni cutar ta kama! A yadda na ji, na shiga cikin wani tashin hankali, domin ni a rayuwa ta ban taɓa ganin irin wannan yanayin ba, don haka sai na shiga cikin wani yanayi.

“Na ce, ‘Mun shiga uku! Abin da mu ke jin sa a nesa, yau ga shi ya zo gare mu, Allah ka kawo mana ɗauki.’

“Wallahi na shiga tashin hankalin da ban taɓa shiga ba, domin yaron tuƙin jirgin sama ya ke, ya baro Abuja, ya na zuwa Gombe sai kawai aka killace shi aka ce ya kamu da cutar.

“To kuma Allah ya kawo mana sauƙin abin, domin bayan kwana takwas da aka ƙara gwada shi sai aka ce an gano ba ya ɗauke da cutar.

“Sai daga nan na fita daga cikin tashin hankalin da na shiga

“Amma dai wannan cutar ko ba ta kama ka ba, ka ji an ce wani naka ya kamu da ita, to ji za ka yi kamar ta same ka. Don haka ina roƙon Allah ya kawo mana ƙarshen wannan cutar, domin ni tun da na ke ban taɓa shiga cikin tashin hankali kamar na wannan lokacin ba.”

Daga ƙarshe Zahra’u ta yi kira ga jama’a da su rinƙa kiyaye kan su da kuma bin dokokin da hukumomin lafiya su ka tsara domin kauce wa yaɗuwar cutar a cikin al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here