Jahar katsina ta sake rufe makaratun Allo, islammiya, haramta yin bara da Kuma taro

0
239

Daga Hannatu Suleiman Abba

Gwamna jahar katsina Aminu Bello masari ne ya bayyana haka a wata takarda da ya rabawa manema labarai, ta hannu sakatarin gwamnatin jahar inda ya Kara umarta da a cigaba da rufe duk wani makaratun islamiyya, Allo,haramta yin bara da taro a fadin jahar.

Gwanna Katsina ya bada wanna umarni ne a yau ranar Alhamis Sha Daya ga wata Juli, shekara ta dubu biyu da ashiri bayan wata ganawa da yayi da hukomin tsaro,Malaman Addini,sai kuma wasu mambobi dake Kula da dakile Annobar Corona biros a jahar da kuma ruwa da tsaki a jahar a dakin taro Muhammad buhari dake gidan gwannatin jahar katsina.

Inda yakara dacewa, gwannati jahar katsina ta lura Da cewa Malaman dake koyarwa a makarantun islamiyya da na Allo sun bude biyo bayan sausauta dokar zaman gida da gwamnatin tayi Wanda haka ya bawa malaman damar ci gaba da gudanar da koyarwa ,bayan kuma dokar rufe makaratun a jahar na na,Yayin da na take gwanna ya bada umarni ga jami’an tsaro jahar dasu Kama duk wanda aka Kama ya yayi burus da dokar.

Hakazalika , gwanna Bello ya Kara haramta yin bara akan tituna a jahar inda yace duk Wanda aka Kama yana yin bara za a hukunta shi ko Kuma iyayensa,Wanda ya kara Jan hankalin yan jahar ta katsina da su cigaba da bin dokar da hukomomin lafiya da na jami’an tsaro suka bayar ta hanyar saka takukumin fuska,bada tsazar a cikin mutane,yawaita wanke hannu da sabulu ko sinadarin wanke hannu da Kuma kauracewa tararuka.

A karshe Gwanna jahar katsina Aminu Bello masari ya ce gwannati jahar zata yi iya Mai yiwa waje gani ta sausauta dokar ,inda taga yadda halin Annobar Corona biros ta kasance a jahar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here