Anyi Zanga-zanga Kan Matsalar Tsaro A Katsina

0
159

Daga Hannatu Sulaiman Abba

Masu zanga-zangar da suka cika titina makil, sun kulle titin da ya yi iyaka da Funtua da Faskari da manyan itatuwa da duwatsu, sakamakon harin da aka sake kaiwa a yankin Faskari a jiya.

Zanga-zangar dai ta biyo bayan zargin rashin daukar kwararan matakai da gwamnatin Katsina da ta tarayya ta kasa yi kan yawaitar kashe-kashen da ake yi a wasu yankunan jihar ta Katsina, inda a shekaran jiya Talata an kashe mutane 52 a yankin Kadisau, sannan kuma a jiya ma an sake kawo farmaki inda aka samu gawarwaki 12 a yau.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here