A Fara Biyan Malaman Allo Albashi ….Dr Abdulkadir koguna

0
674

Daga Hannatu Suleiman Abba

Sarki hausawa afrika kuma Sardauna Agadaz Dakta Abdulkadir Labaran Koguna ne ya bayyana haka ga jaridar PRIME TIME Inda yace tun kafin zuwan ilimi Boko malamai Addini ke fama da kuma jajajircewa wajen gani kasar Hausa ta fita daga halin jahilci a waccen lokacin Domin Samun ci gaba a yakin kasar.

Dakta Koguna yace dole ne Gwannati jahar kano ta waiwaye malamai Addini mussaman masu koyarwa ta fanni Tara Almajiri Wanda aka fi Sani da karatun Allo,inda yace “ko da wata jahar batayi ba to kamata yayi jahar kano ta fito da tsarin saka malaman dake koyar wa a makarantun Allo cikin Jeri sahun masu karbar Albashi kamar yadda Malaman dake koyarwa a makarantun Boko ke samu ko da ace an samu hutu a makarantun,Domin duk wani dake takama da ilimin Boko ko wani mukamin a Gwannati a wanna zamani toh sai da yafara da makarantar Allo”

Hakazalika,Sardauna agadaz din ya nuna takaicin sa kan yarda malamai makarantar Allo ke cikin wani yanani biyo bayan bullar Annobar Corona biros a kasar na,Wanda yace Malaman ka samu kudin da suke Kula da iyalan su ne ta fanni karbar kudi laraba inda kudi baya wuce naira 10 a duk sati daga gun kowanne dalibi.

Dakta koguna ya Kara dacewa ,rashin Kula da Malaman na makaratun Allo a jahar na ,na iya sa su shiga cikin wani mawuyacin halin ,Wanda a sanadiyyar haka zai gifa su cikin sahun masu bara a jahar da aka haramta yin.

A karshe, Sardauna Agadaz kuma sarki Hausawa Afrika Dr Abdulkadir Labaran Koguna ya shawarci Gwannati jahar Kano da ta Kara duba muhimmacin ilimin muhammadiya a kasar Hausa bawai ta karka akan ilimin Boko ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here