Coronavirus a Kaduna: El-Rufai ya sassauta dokar hana fita

0
123

Daga Hannatu Sulaiman Abba

Gwamnatin Kaduna da ke Najeriya ta sassauta dokar kullen da ta saka a jihar wadda ake kallo a matsayin mafi tsauri a arewacin kasar.

Gwamna Nasir Ahmed El-Rufai ne ya sanar da hakan a wani jawabi da ya yi ga jihar ranar Talata, inda ya ce a karon farko cikin makonni masu yawa za a bar masallatai su yi sallar Juma’a sannan majami’u su gudanar da ibada ranar Lahadi.

Gwamnan ya kuma sassauta dokar hana zirga-zirga a jihar amma a yanzu babu fita daga ƙarfe 8:00 na dare zuwa 5:00 na asuba.

Wannan sassaucin zai fara aiki daga Laraba 10 ga watan Yuni.

Gwamna El-Rufai ya ce bisa ƙa’idojin da gwamnati ta shimfiɗa, wuraren sana’a za su iya buɗewa sannan su samar da na’urar auna zafin jikin mutum.

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce kuma za a bai wa masallatai damar budewa domin ibada a ranar Juma’a kadai sai kuma coci-coci a ranar Lahadi.

Sai dai gwamnan ya ce ba za a bude kasuwanni ba tukunna.

Ya ƙara da cewa sa’o’in aiki za su riƙa farawa daga 9:00 na safe zuwa 3:00 na rana.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here