Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa a fadar shugaban kasa

0
135

Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa a fadar shugaban kasa Hakkin mallakar hoto: Fadar shugaban kasa

 

An zabi sauya salon zaman majalisar ne ta hanyar ba da tazara domin kiyaye dokokin da mahukuntan lafiya suka shar’anta da manufar dakile yaduwar cutar korona da ta zamto ruwan dare. Tun da misalin karfe 10.00 na safiyar Laraba aka fara zaman majalisar a babban dakin taro da ke fadar shugaban kasar wato Council Chambers.

 

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, sakataren gwamnatin tarayya, Mista Boss Mustapha, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari sun halarci zaman.

 

Babban mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasa, Babagana Monguno, shi ma ya halarci zaman majalisar.

 

Ministocin da a dole su na da ta cewa kuma su na dauke da bayanan da za su gabatar su ne kadai suka halarci zaman majalisar a zahiri.

 

An tattaro cewa, ministoci goma sun halarci zaman ta hanyar bidiyo a fafutikar da ake ci gaba da yi ta kiyaye dokar nesa-nesa da juna. Ministocin da suka halarci zaman a zahiri sun hadar da na Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, Ministan Lantarki, Saleh Mamman, Ministan Labarai da Al’adu, Lai Muhammad. Sauran sun hadar da Ministar Kudi Kasafi da Tsare-Tsare; Zainab Ahmed, Ministan Harkokin cikin Gida; Ogbeni Rauf Aregbesola, Karamin Ministan Neja Delta; Sanata Omotayo Alasoadura. Sai kuma Ministan Ruwa; Injiniya Suleiman Adamu, Ministar Harkokin Mata; Dame Pauline Tallen, da kuma Ministan Neja Delta; Sanata Godswill Akpabio.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here